Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ta shirya bikin yaye ɗalibai kimanin 22,932. Shugaban jami'ar Farfesa Suleiman Bilbis ne ya bay...
Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ta shirya bikin yaye ɗalibai kimanin 22,932.
Shugaban jami'ar Farfesa Suleiman Bilbis ne ya bayyana haka a yayin taron yaye ɗaliban da jami'ar ta shirya, a babban ɗakin taron jami'ar.
Ya ƙara da cewa daga cikin ɗaliban, akwai waɗanda za su samu digirin digirgir, da digiri na biyu, da kuma digiri na farko.
Wakilinmu da ke wurin ya ce taron ya samu halartar manyan baƙi daga cikin wajen jihar Sakkwato.
No comments