Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Ɗauki Mataki Kan China Kan Tallafa Wa Rasha A Yaƙin Ukraine - Blinken

  Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya shaida wa BBC cewa, a shirye Amurka take ta ɗauki matakai kan China idan har ta ci gab...

 


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya shaida wa BBC cewa, a shirye Amurka take ta ɗauki matakai kan China idan har ta ci gaba da bai wa Rasha kayayyakin da take amfani da su wajen yaƙin da take yi a Ukraine.

Da yake jawabi bayan tattaunawa da shugaba Xi Jinping, Mista Blinken ya ce, ya bayyana ƙarara cewa, China na taimakawa wajen ƙara rura wutar babbar barazana da tsaron Turai ke fuskanta tun bayan kawo ƙarshen yaƙin cacar baka.

Mista Blinken ya ce China ce ke samar da kashi 70 cikin dari na injuna da kuma, kashi 90 cikin dari na na'urorin lantarki da Rasha ke samu daga ƙasashen ƙetare.

Sakataren wajen na Amurka bai bayyana matakan da Amurka ke shirin ɗauka kan Chinar ba.

No comments