WaÉ—anda suka shirya gangamin nuna goya baya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun ce babu gudu ba ja da baya sai sun gudanar da taronsu kamar ...
WaÉ—anda suka shirya gangamin nuna goya baya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun ce babu gudu ba ja da baya sai sun gudanar da taronsu kamar yadda suka shirya.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar, Douye Diri ya hana taron, inda ya ce taron zai tayar da zaune tsaye ne a jiharsa, kuma ba zai bar hakan ya faru ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana a wani taron dattawa da jami'an tsaron jihar cewa bai amince a gudanar da taron ba a jiharsa.
Amma a wata sanarwa da kakakin sakataren jam'iyyar PDP na yankin kudu maso kudu, George Turnah ya fitar, wanda shi ne yake jagorantar shirya gangamin, ya ce babu gudu babu ja da baya.
Turnah ya ce siyasar ƙabilanci ba ta mazauni a siyasar Najeriya, inda ya ƙara da cewa suna da ƴancin shirya gangami na lumana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya ce ba su da wata manufar tayar da zaune tsaye, inda ya ƙara da cewa za su shirya gangami ne kawai domin nuna goyon bayansu ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Nyesom Wike.
No comments