Karanta labarin nan; YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata A Zamfara Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ba da umarnin rufe da...
Karanta labarin nan; YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata A Zamfara
Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ba da umarnin rufe daukacin makarantun kwana dake jihar hakan ya biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kai har suka yi awon gaba da daruruwan dalibai a makarantar sakandaren 'yan mata ta GGSS Jangebe.
Karanta labarin nan; Iyayen Dalibai Mata Da Aka Sace A Jihar Zamfara Sun Yi Kukan Kura Sun Shiga Daji Neman 'Ya'yansu
Karanta labarin nan; Dalibai Mata 317 Ne 'Yan Bindiga Suka Sace A Makarantar Jangebe -Kwamishinan 'Yan Sanda
A jawabinsa ga jama’ar jihar a ranar Juma’a, Gwamnan ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa. Inda ya ce; “’yan’uwana mutanen jihar Zamfara wannan ba lokaci ba ne na zargin juna. Sarkakiyar da muka shiga a kwanan nan daga ’yan ta’adda na bukatar a yi amfani da salo daya a dukkannin jihohin da abin ya shafa; Babbar mafita daga kalubalen ita ce daukar matakin da ya dace na bai daya”, inji shi.
Sannan ya ci gaba da cewa; “bai kamata siyasa ko bambancin ra’ayi ya hana ruwa gudu ba wajen yaki da matsalar tsaro. Manufar gwamnatinmu ita ce tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin jama’a kuma ba ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin”, ya tabbatar.
Ya karkare da kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu su kuma ba wa miyagun da ke son yin amfani da halin da ake ciki a yanzu don cimma burin siyasa kunya. Inda ya kara da cewa; “insha Allah za mu ga bayan wannan yanayin da muke ciki,” inji shi.
No comments