Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubuakar ya ce jiharsa na da kudin da za ta iya biyan ma'aikatanta duk da barazanar NNPC na ce...
Gwamnan
Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubuakar ya ce jiharsa na da kudin da za ta iya
biyan ma'aikatanta duk da barazanar NNPC na cewa ba zai bayar da kosisi ba daga
asusun tarayya da da ake rabawa jihohi kamar yadda BBC ta labarto.
Gwamnan
ya ba da tabbacin ne yayin da yake yi wa ma'aikata jawabi a dakin taro na
Ahmadu Bello da ke Dutse babban birnin Jihar, a wani bangare na bikin ranar
ma'aikata ta duniya.
Sannan
ya tabbatar wa da ma'aikata jajurcewarsa na biyan naira 30,000 a matsayin mafi
karancin albashi a watanni masu zuwa duk da barazanar da kamfanin mai na NNPC
ya yi cewa ba zai saka kudi a asusun gwamnatin tarayya ba a wata mai zuwa.
"Ma'aikata
su kwantar da hankalinsu za mu biya su albashinsu kamar yadda aka saba kuma
akan lokaci".
"An
sha zargina da boye kudi ba tare da kashe su ba, amma mu mun san irin wannan
lokacin yana zuwa, kuma ga shi ya zo," a cewarsa.
"Lokacin
da muka zo mun san wammam lokacin na zuwa da ba za mu samu komai ba daga
gwamnatin tarayya saboda faduwar farashin mai, bugu da kari annobar korona ta
kara jefa tattalin arzikin kasar cikin wani mawuyacin hali" in ji Badar
No comments