Daga Muhammad Farouk Dan majalisar jihar mai wakiltar Batsari, Alhaji Jabiru Yusufu Yau-Yau ya tsallake harin ‘yan bindiga kamar yadd...
Daga Muhammad Farouk
Dan majalisar jihar mai wakiltar Batsari, Alhaji Jabiru Yusufu
Yau-Yau ya tsallake harin ‘yan bindiga kamar yadda Katsina City News ta labarto
Alhaji Jabiru Yau-Yau ya tsallake harin ‘yan
bindigar ne a daidai kauyen Garwa a lokacin da ya je ziyarar ta’aziyyah.
Wakilin Katsina City News ya labarto cewa Alhaji
Jabiru Yau-Yau ya ce ‘yan kauyen sun shaida masa cewa ‘yan leken asirin masu
garkuwa da jama’ar ne suka shaida musu zuwansa, shiyasa suka zo akan Babura suka
tare hanyar da ya shiga kauyen. Wanda hakan ya sanya wadansu ‘yan kauyen da
suka ga abin da ya faru suka shaida masa da cewa ya canza hanya idan ya tashi
komawa.
A yayin da ‘yan bindigar suka yi zaman jiran
dakon Alhaji Jabiru Yau-Yau ya bayyana ta hanyar da suka tare domin su yi
garkuwa da shi, ko su kashe shi, amma ba tare da sun sani ba tuni ya sauya
hanyar ta daji ya koma inda ya fito tare da rakiyar jami’an tsaron da yake tafe
da su.
No comments