Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnonin Kudancin Nijeriya Na Son Buhari Ya Gaggauta Kiran Taron Kasa Kan Tsaro

Gwamnonin Jihohi 17 da suka fito daga kudancin Nijeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kiran taron kas...



Gwamnonin Jihohi 17 da suka fito daga kudancin Nijeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kiran taron kasa da zai tattauna halin da kasa ke ciki da kuma yiwa jama’a jawabi domin su fahimci abinda ke tafiya dangane da matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar.

Gwamnonin sun kuma amince a tsakanin su da haramta kiwo a daukacin jihohin dake kudancin kasar saboda abinda suka kira matsalolin tsaron da kiwon ke haifarwa.

Gwamnonin sun dauki wannan matsayi ne lokacin da suka gudanar da taron su a Asaba dake Jihar Delta domin tattauna batutuwan da suka shafi Jihohin su da kuma kasa baki daya.

Kafin dai wannan lokaci, daidaikun Jihohin sun yi dokar haramta kiwon wanda akasari Fulani makiyaya daga arewacin kasar keyi, saboda rikice rikicen da aka dinga samu a baya bayan nan wanda ke kaiga rasa rayuka musamman tsakanin manoma da makiyayan.

No comments