Shugabannin zauren hadin kan Malaman Jihar Kano sun ce sun fuskanci 'ba da gaske gwamnatin Ganduje take ba kan muhawara da Sheikh Ab...
Shugabannin
zauren hadin kan Malaman Jihar Kano sun ce sun fuskanci 'ba da gaske gwamnatin
Ganduje take ba kan muhawara da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara' kamar yadda
BBC Hausa suka labarto.
Yayin
wani zama da suka yi wanda Dakta Saidu Dukawa wanda daya daga cikinsu ya
wallafa a shafinsa na Facebbok, yace sun fitar da matsaya game da jan kafar da
gwammatin Kano ke yi kan zaman da aka fara tsarawa na tuhumar da za a yii wa
Sheik Abduljabbar Naisru Kabara na zargin 'cin zarafin da ya ke yi wa Manzon
Allah da Sahabbansa'.
Sun
yi bayanin matakan da suka dauka a baya na rubuta wa gwamnati wasika har guda
uku, daya zuwa ga hukumar shari'a daya kuma zuwa ga kwamishinan sharia, guda
kuma zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano Ganduje kai tsaye.
Dukawa
ya rubuta cewa "amman tsawon wata uku babu amsar ko daya daga ciki
wasikun, a don haka, Malaman sun bukaci duk wanda ya ke neman bayani game da
maganar to ya nema a wurin gwamnati" Dukawa ya rubuta.
Haka
kuma an bukaci "al'umma su dukufa da addua cewar duk wanda ya taba
mutuncin sahabbai da wanda ya goyi bayansa, Allah Ta'ala ya yi mana
maganinsa".
No comments