Daga Fatima Idris, Zariya A ranar 30 ga watan Agustan 2021 aka gudanar da zaben sabbin shugabanni bayan cikar wa'adin wanda suke k...
Daga
Fatima Idris, Zariya
A
ranar 30 ga watan Agustan 2021 aka gudanar da zaben sabbin shugabanni bayan
cikar wa'adin wanda suke kai a baya.
Zaben
an gudanar da shi ne a filin Kwantagora dake harabar Jami'ar. Shi ne mukami
mafi girma ta dalibai.
A zaben
na wannan lokacin, mutum bakwai suka fafata domin neman shugabancin kujerar.
An
fitar da kuri'u guda 79 cikin ikon Allah Dalibi mai suna Jibrin Idris daga
jihar Zamfara a Tsangayar Ilmin Kimiyyar kasa (Science Education Geography),
inda ya sami nasarar cinye zaben bayan kada mutane 6 da samun kuri'u 27 wanda
hakan ya ba shi damar zama shugaban daliban Jami'ar na Ahmadu Bello Zariya baki
daya.
Farfesa
Ibrahim Dabo daga sashen Kimiyyar Sinadarai shi ya shugabanci zaben kuma ya
shaidawa manema labarai cewa ya ji dadin yadda daliban suka bi dukkan sharudan
zaben kuma ya yi fatan alheri gare su.
Kwamared
Jibril zababben shugaban ya bayyana jin dadinsa bisa yadda dalibai suka bashi
goyan baya.
Kuma
ya yi alkawari zai cikawa dalibai dukkan alkawarin da ya dauka kuma ya ce zai
kare masu hakkokinsu.
Karshe
ya yi kira da hukumar tsaro na Jami’ar da su dage wajen kare rayukan dalibai
kamar yadda suka saba.
Hi my name is Aminu Bundu please I'll like to reach out the management
ReplyDeleteContact madogaratv@gmail.com or call 08064613705
Delete