Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jinjina Ga Mohammed Bello Koko: Gwarzon Bunƙasa NPA

Daga Bello Hamza, Abuja Nijeriya na fuskantar ci gaba a sassa da dama, dole a mika godiya da yabo zuwa ga wasu jajirtattun mutan...


Daga Bello Hamza, Abuja

Nijeriya na fuskantar ci gaba a sassa da dama, dole a mika godiya da yabo zuwa ga wasu jajirtattun mutane masu hange nesa. Mohammed Bello Koko, shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) na xaya daga cikinsu, shi ne a kan gaba wajen sauya fasalin hukumar NPA tun da ya zama shuugabanta a watan Fabrairu na shekarar 2022.

A karkashin shugabancin Mohammed Bello Koko NPA ta zama a kan gaba wajen tabbatar da qwarewa a aikin gwamnati da kuma aiki ba tare da wata mastala, ana iya tabbatar da wannan ne in aka lura da nasarar kashi 100 a cikin 100 da NPA ta samu wajen aiwatar da sauye-sauye a bangaren tashoshin jiragen ruwa a fadin Nijeriya dama duniya baki daya.

Cikin manya-manyan sauye-sauye da aka samu a karkashin jagorancin Mohammed Bello Koko shi ne yadda aka rage lokacin da ake batawa wajen shirye-shiryen fitar da kayayyaki wajen kasar nan daga kwanaki 10 zuwa akalla kwana 3 zuwa 5. Wannan matakin ya yi matukar daukaka darajar Nijeriya a kasuwar duniya ya kuma samar da sauki ga masu harkokin kasuwanci da tashoshin jiragen ruwan Nijeriya ba kamar yadda abin yake ba a shekarun baya.

Sauye-sauyen da Mohammed Bello Koko yake gabatarwa a NPA ya wuce na yanzu-yanzu nan, a halin yanzu ya fuskanci gyare- gyaren da za a fuskanci dogon lokaci ana amfana dasu musamman yadda aka kafa wurare a cikin teku wanda zai taimaka wa Nijeriya shiga cikin jerin kasashe masu amfana da tattalin arzikin teku a duniya, wanda hanya ne na bunkasa tattalin arzikin kasa gaba daya.

Zamanin shugabancin Mohammed Bello Koko an samu bunkasar kudin shigar NPA na irin da ba a taba gani ba a tarihin hukumar. Lamarin ya tashi daga Naira Biliyan 361 a shekarar 2022 zuwa Naira biliyan 501 zuwa karshen shekarar 2023.

Haka kuma Mohammed Bello Koko ya yi maganin mastalar da ta yi shekaru tana addabar NPA wato cunkoso a tashar jiragen ruwan Legas, a halin yanzu an samu sauki, ana kuma mu’amala a tashoshin ba tare da wata mastala ba. Tabbas wannan mutumin yana tafiyar da lamarinsa daidai da manufofin tattalin arzikin shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunkasa dukkan sassan Nijeriya.

No comments