Daga Bello Hamza Abuja Ministan tattalin arzikin teku, Adegboyega Oyetola, ya jagoranci bikin kaddamar da sabbin kananan jiragen...
Daga Bello Hamza Abuja
Ministan tattalin arzikin teku, Adegboyega Oyetola, ya jagoranci bikin kaddamar da sabbin kananan jiragen ruwa guda biyu don karfafawa tare da saukaka zirga-zirga a tsakanin matatar man Dangote da tashar jiragen ruwa na Lekki. An sanya wa jiragen ruwan sunan MT IRAGBIJI da MT BAMA.
Ana sa ran jiragen za su taimaka wajen sintirin jami’an tsaro a tsakanin matatar man Dangote da tashar jiragen ruwa na Lekki.
A jawabinsa, Ministan ya ce, an dauki mataikin samar da jiragen ruwan ne don karfafa matsayin Nijeriya a cikin kasashen duniya masu hada-hadar da teku a yankin Afrika.
Ya ce, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tsayu wajen ganin an karfafa kaddarorin Nijeriya da ke cikin teku.
Tun da farko, a jawabinsa Shugaban Hukumar Tashoshin JIragen Ruwan Nijeriya NPA, Mohammed Bello-Koko, ya ce, samar da jiragen ruwan daukaka matsayin Nijeriya a tsakanin kasashen yankin Afrika masu mu’amala da teku.
Ya kuma bayyana cewa, za a yi amfani da jiragen ruwa a tsakanin matatar mai na Dangote da kuma tashar jiragen ruwa na Lekki wannan a yanzu ta zama babbar fata ga Nijeriya wajen bunkasar tattalin arzikinta, musamman ganin tana gab da fara tace gangan mai 650,000 a rana.
No comments