Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Magajin Ali Ƙwara, Unkuji Ya Gargaɗi Batagarin Matasan Azare

Daga Idris Ibrahim Azare Magajin Ali kwara, wanda ya ƙware wajen taimaka wa 'yan sanda a daƙile manyan barayi 'yan fashi da makami a...



Daga Idris Ibrahim Azare

Magajin Ali kwara, wanda ya ƙware wajen taimaka wa 'yan sanda a daƙile manyan barayi 'yan fashi da makami a sassan ƙasar nan don kawo zaman lafiyar al'umma, Alhaji Ahmad Muhammad Ƙwara, wanda aka fi sani da Unkuji, ya bayyana cewa a 'yan kwanakin da suka gabata ya samu kiraye-kiraye daga Jama'ar garin Azare ta jijar Bauchi domin ya kawo masu ɗauki sakamakon yadda yara matasa batagari suke addabar su da ƙwacen waya da balle shaguna da haura gidaje, da sauran ire-iren waɗannan laifuka.

Don haka Unkuji ya gargaɗi matasan masu wannan halin, da cewa kowa ya shiga taitayin sa, wanda in ba haka ba, zai sa ƙafar wandon ɗaya da duk wani ƙarami ko babban barayo marar kunya.

Don haka ya ce, wannan gargaɗi ne ga iyayen yara da cewa in ya kama yaro, sannan wani Uba ko ɗan uwa ya biyo sayu gidansa, to ya yi ta kansa, don har shi zai haɗa da shi.

Yana mai ƙorafin cewa iyaye sun ƙi kula da 'ya'yansu, sun sanya soyayya ga yaransu,ba sa faɗa musu gaskiya da ba su tarbiyar da Allah ya ɗora musu. Jarumin ya ƙara da cewa, yanzu suna nan sun sa ƙasar a gaba suna gumurzu da manyan barari masu manyan bindiga a lungu da saƙo na ƙasar nan, musamman a wasu jihohi da suke addabar Jama'a, kuma Ana samun nasarori wajen daƙile su.

Ya kuma ƙara da cewa zai gyara cikin garin Azare ta yadda zai cafke masu sayar da taba da ƙwayoyi da sauran aboben shaye-shaye da matasan ke sha. A ƙarshe Unkuji ya yi kira ga tsagerun matasan da su jefar da makaman su su rungumin sana'a, domin idan suka ci karo da shi, to abin da zai biyo baya ba zai yi daɗi ba.

Ya ce, in kuma rashin abin yi ne yake sa matasan aikata wannan abu, to ya yi Alƙawarin cewa su kawo kan su, zai tallafa masu da ƙaramin jari don su zama nagari, subar garin ya zauna Lafiya. Garin na Azare dai ya faɗa cikin wani yanayi da wasu matasa ke ƙwacan wayoyi da baburan hawa, tare da haura gidajan mutane suna ƙwatar duk abin da suka ci karo da shi.

No comments