Daga Zainab Rauf, Abuja Harkar Musulunci a Nijeriya ta yi kakkausar suka da Allah-wadai da kama Ramzy Ibrahim Abusafiah, shugaban al’ummar...
Daga Zainab Rauf, Abuja
Harkar Musulunci a Nijeriya ta yi kakkausar
suka da Allah-wadai da kama Ramzy Ibrahim Abusafiah, shugaban al’ummar Falasɗinu
da ke Nijeriya, inda ta bukaci a sako shi ba tare da wani sharadi ba, kuma nan
take.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar
Laraba, 27 ga Agusta, wadda Sheikh Sidi Munir Mainasara Sokoto ya sanya wa
hannu a madadin jagoran Harkar, Sayyid Ibraheem Zakzaky, ta bayyana wannan kamu
a matsayin “abin ƙi, abin Allah-wadai kuma abin da zai iya bata sunan Nijeriya
a idon duniya.”
A cewar sanarwar, jami’an tsaron Nijeriya
ne suka kama Abusafiah a ranar Juma’a, 22 ga Agusta, 2025. Duk da cewa ba a
fitar da wata hujja a hukumance dangane da dalilin kamewar ba, Harkar Musulunci
na ganin hakan na da nasaba da wata sabuwar yarjejeniyar tsaro tsakanin Nijeriya
da Isra’ila—yarjejeniya da Harkar ta soka ƙwarai.
“Wannan kamu... ta bayyana sabon
salo a siyasar diflomasiyyar Nijeriya,” in ji sanarwar. “Wannan saba wa goyon
bayan da Nijeriya ke bai wa Falasɗinu ne a tsawon tarihi, kuma haɗari ce babba da
ke nuna goyon baya ga wata haramtacciyar ƙasa da ake ƙin amince mata a duniya.”
Harkar Musuluncin ta tunatar da
jama’a irin goyon bayan da Nijeriya ta ba Falasɗinu a tarihi, ciki har da
amincewar Nijeriya da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci a shekarar
1988, da kuma ƙuri’ar da ta kaɗa a Majalisar Ɗinkin Duniya a 2012 don bai wa
Falasɗinu ‘yanci da matsayinta. Haka kuma, ta ambato wata sanarwa daga Ministan
Harkokin Waje na Nijeriya, Yusuf Tuggar, a shekarar 2024, inda ya yi
Allah-wadai da hare-haren Isra’ila a Gaza yayin wata ziyarar diflomasiyya da ya
kai ƙasar Qatar.
Harkar Musulunci ta nuna damuwa kan
abin da ta kira “canjin fuska” a harkar diflomasiyyar Nijeriya a ƙarƙashin
shugabancin Bola Ahmed Tinubu, musamman duba da sabuwar alaƙar Nijeriya da abin
da Harkar ta nanata da “haramtacciyar ƙasar Isra’ila.”
Sanarwar ta yi nuni da yadda
ƙasashen duniya ke ƙara yin Allah-wadai da halayen Isra’ila a Gaza, ciki har da
ƙarar kisan kare dangi da Afrika ta Kudu ta shigar da ita gaban Kotun Ƙoli ta
Duniya (ICJ), tare da goyon bayan wasu ƙasashe da dama. Haka kuma, ta ambaci
takunkumin tattalin arziƙi da ƙasashe kamar Turkiyya da Birtaniya suka ɗora wa
Isra’ila a matsayin wata shaida ta yadda ƙasar ke kara fadawa halin kaɗaituwa.
Baya ga bukatar a saki Abusafiah nan
take, Harkar Musulunci ta kuma bukaci a gaggauta soke duk wata yarjejeniyar
tsaro tsakanin Nijeriya da Isra’ila, tana zargin cewa Isra’ila na amfani da faɗace-faɗacen
Afrika domin sayar da makamai da gudanar da leƙen asiri.
“A don haka, muna kiran malamai, marubuta, ‘yan jarida da daukacin ‘yan Nijeriya da su fito fili su nuna rashin amincewa da wannan sauyin fuska a diflomasiyyar Nijeriya,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta kuma yi kira ga al’ummar
Musulmi da su yi amfani da wannan wata mai albarka na Rabi’ul Awwal—wata da aka
saba amfani da shi wajen haɗin kai da tunani—domin nuna adawa da wannan kamu,
tare da goyon bayan ƙudurin ‘yancin Falasɗinu. Bikin Mauludi na bana, wanda
taken sa shi ne “Haɗa kan Musulmai Wajen Goyon Bayan Falasɗinu”, ana sa ran zai
ƙara ƙarfafa wannan kira.
No comments