Daga Abubakar Musa Zariya Da safiyar yau Talata ne ƙungiyar manya da ƙananan ma'aikatan jami'ar Ahmadu Bello Zariya SSA...
Daga Abubakar Musa Zariya
Da safiyar yau Talata ne ƙungiyar manya da ƙananan ma'aikatan jami'ar Ahmadu Bello Zariya SSANU da SANU suka gudanar da zanga-zangar ƙorafi a cikin harabar jami'ar dake Samaru Zariya.
Jerin Gwanon sun fara ne daga dandalin Mamman Kwantagora zuwa babbar hanyar mashigar jami'ar.
Kwamred Muhammad Yunusa shugaban kungiyar ta SSANU kuma shi ne shugaban gamayyar ƙungiyoyin dake fafutikar.
A yayin da yake gudanar da jawabinsa a cikin dubban 'ya'yan ƙungiyar da suka taru don nuna damuwarsu ga halin da suke ciki da yasa suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu a wannan ranar.
Kwamred Yunusa ya ce sun fito ne saboda bin umurnin uwar ƙungiyar su ta ƙasa domin nuna damuwarsu akan rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya take yi game da Haƙƙoƙin su da suke binta da ya haɗa albashi da wasu alawas alawus da suke bi na watanni 4 da suka gabata.
Kwamred Ynusa ya ce a kwanakin baya sun je yajin aiki bisa matsaya da aka yi da gwamnatin tarayya yasa suka dawo da nufin za a share masu hawayensu ya ce amma abin mamaki sai aka sharewa wasu hawayensu amma su akayi ko in kula dasu koken nasu yace, hakan bai daceba.
Don haka shugaba ya ce "wannan fitowar ta nuna gargaɗine idan ba'a biya mu hakimmuba gaba kaɗan zamuje yajin aikin gargani in basu dauki mataki bayanmu harƙoƙinmuba to tabbas ƙungiya za ta ɗauki mataki na ƙarshe na zuwa yajin aiki mafi girma na ƙasa baki ɗaya" acewarsa
Ƙarshe ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinibu da cewa ya dena kula masu hana ruwa gudu dake ƙoƙarin cin amanar ƙasa dake cikin gwamnatin sa .
Ya ce ƙungiyar SSAN da NASU ƙungiyoyi ne da suke riƙe da ƙasa baki ɗaya domin duk wanda zai yi aikin gwamnati musamman Jami'a to sai ya biyo ta gaban kungiyar saboda muhimmanci su
Kuma ya ƙarkare da yin jinjina ga gamayyar ƙungiyoyin da suka bayar da haɗin kai suka fito suka nuna goyon baya tare da bin duk dokokin kungiyar
An yi lafiya an tashi lafiya.
No comments