Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙaruwar Harajin Da Gwamnati Ta Sanya Ne Ya Janyo Hauhawar Farashin Kayayyakin Masarufi - Cewar Kuchi

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar ƙaruwar harajin da gwamnati ke sanyawa ne ya janyo hauhawar farashin kayan masarufi. ...

Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar ƙaruwar harajin da gwamnati ke sanyawa ne ya janyo hauhawar farashin kayan masarufi. Domin gwamnati ta mayar da 'yan kasuwa gugar yasa, yadda ta ga dama haka take kakabawa yan kasuwa. 

Wani matashin ɗan kasuwa mai sana'ar burodi, Alhaji Zakari Muhammad Kuchi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna.

Kuchi, ya ci gaba da cewar maganar hauhawar farashin kaya laifin gwamnati ne domin harajin da yan kaauwa ke biya yanzu abin ya wuce hankali, saboda haka maganar bunkasa kananan masana'antu da gwamnatin nan ke ikirari ba gaskiya ba ne.

Maganar da ni ke yi daku yanzu haka, duk dan kasuwan da ka san yana da jarin miliyan biyu zuwa uku bai da cikakkiyar jarin dubu dari biyar yanzu. Misali a sana'ar mu na burodi, wanda fulawa da suga a kasar nan ake yin su,  a kullu yaumin idan muka buga burodi muka fitar cinikin da za mu yi ba zai mayar da irin aikin da aka yi a baya ba, sana'a yanzu ana yin ta ne rage takaicin zaman rashin aikin, shi yasa duk kokarin da muke yi shi ne kar jarin mu ya lalace.

Da ya juya kan farfagandar samun nasarar shugaba Tinubu zagaye na biyu, wannan mafarki ne, domin da irin halin da talakan kasar nan ke ciki yan farfaganda ke yaudarar kan su, waye a cikinsu zai iya komawa mazabarsa ya tallata Tinubun, balle ya kawo mai mazabarsa. Wannan farfaganda ce kawai da rashin abin yi, amma halin da talakan kasar nan ke ciki na tsadar rayuwa da rashin tsaro ma ya ishe shi domin gwamnatin a kullun kara damalmalewa take yi.

Da ya juya kan gwamnatin Neja kuwa, matashin ya shawarci makusantan gwamnatin jiha, ta waiwayi halin da talakawan da suka zabe ta ke ciki, dubban talakawa ke kwana ba su ci ba, kuma ba su san mafitar rayuwa ba, amma an wayi gari muna jin gwamna na rabawa yan yiwa hidimar kasa dubu dari biyu-biyu, yayin da talakan da ya yi zaben ke cikin kuncin rayuwa.

Ya kamata ayyukan da gwamna ya sanya kudurin aiwatarwa ya kamata ya dubi yan siyasar da suka wahala da shi da ke kusa da al'umma ya taimaka masu da ayyuka ta yadda zasu taimaka masa wajen tallafawa al'ummarsu, ayyukan da ake yi abin a yaba ne, amma komai kyau da inganci idan mutane na fama da yunwa akwai damuwa sosai.

Kuchi, ya shawarci gwamnatin jiha kan yunkurin farfado da harkar noma, da ta tabbatar ta sanya idanu kan yadda ake  fitar da kayan anfanin gona da ta samar dan tallafawa manoma. Domin mun shiga watan shida, amma yanzu haka takin gwamnati sai wanda ke da daurin gindi, kuma dukkanin kayan anfanin gona a yanzu ba sa sayuwa, balle manomi ya samu sassauci.

"Mun samun labarin gwamnatin Bago ta samar da daruruwan motocin noma, amma mutanen karkara da ke noman da gaske ba su san ana yin sa ba. Dan haka ina jawo hankalin maigirma gwamna da ya sanya idanu ya tabbatar mutanen karkara sun mori wannan garabasar".

Matashin, ya jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta nazarci tsarin biyan haraji da kuma illar tsaurara haraji ga kananan yan kasuwa domin yanzu kananan masana'antu da dama sun durkushe.

No comments