Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Moniepoint Na Shirin Korar Ma'aikata Fiye Da Dubu Ɗaya Daga Arewa

Daga Zailani Mustapha   Kamfanin hada-hadar kuɗi na Moniepoint yana shirin korar ma'aikata fiye da dubu ɗaya daga arewa. Ma...


Daga Zailani Mustapha 

Kamfanin hada-hadar kuɗi na Moniepoint yana shirin korar ma'aikata fiye da dubu ɗaya daga arewa. Ma'aikatan masu muƙamin manajan hulɗar kasuwanci (BRM) za su rasa ayyukansu ne sakamakon zarginsu da kamfanin ya yi wajen ƙin bin kwastomomi inda suke domin tantance adireshin su kamar yadda babban bankin Nijeriya, wato CBN ya buƙata. 

Wannan zargin ya fito ne daga bakin wasu ma'aikatan Moniepoint da suka nemi a sakaya sunansu. Inda suka zargi kamfanin da yankan baya. 

CBN ce ta sa a tantance dukkanin adireshin masu asusu dake hulɗa da Moniepoint da dai sauran su. 

Wani jami'in Moniepoint wanda ke riƙe da manajan hulɗar kasuwanci a arewa wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa wakilinmu cewa; "Da farko mu ba su yi mana wani horaswa ba na yadda za a yi wannan aikin. Kawai sun maƙala mana adadin waɗanda za mu yi ne. Mun tantance adireshin mutane, amma ba mu san cewa dole sai ka bi kowa inda yake za ka yi masa ba. Ma'ana kamar ka je gidansu ko shagonsa ko ofis ɗinsa", in ji shi. 

Ya ci gaba da cewa; "ka ga ya kamata su yi mana uzuri akan cewa ba su horas da mu ba. Ya kamata a gargaɗe mu ne sannan sai su yi
mana gyare-gyare. Yanzu abin da suke yi shi ne korar duk wanda ya yi wannan aikin tantance adireshin a wuri ɗaya a maimakon ya bi kowa inda yake ya yi masa. Duk wanda ya yi korarsa suke yi. Babu wani gargaɗi, ba komai".  

"Binciken da muka yi ƴan arewa sun fi yin laifin da yawa akan ƴan Kudu. Akwai waɗanda suka hana a ga shugaban kamfanin wato Tosin, suna so ne kawai a kore mu saboda wannan kuskuren", ya labarta. 

Bayanai sun nuna cewa; idan har ba a dakatar da wannan matakin ba, korar ma'aikatan zai shafi aƙalla mutum fiye da dubu ɗaya. 

Ya tabbatar mana da cewa; "waɗanda ake son a kora sune manajan hulɗar kasuwanci (Business Relationship Manager (BRM)) a arewa kawai. Wannan zai iya karya Moniepoint a Arewa. Saboda duk mai amfani da Moniepoint a arewa zai daina ne ya koma wani kamfanin". 

Rahotanni sun nuna cewa; waɗannan ma'aikatan wato BRM sune suka yaɗa kamfanin Moniepoint a arewa da har yasa ya karɓu a yankin. 

No comments