Kwamitin duban wata a Najeriya ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal, wanda ya kawo ƙarshen azumin watan Ramadan na shekarar 1446/20...
Kwamitin duban wata a Najeriya ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal, wanda ya kawo ƙarshen azumin watan Ramadan na shekarar 1446/2025.
Mai alfarma Sarkin musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ne ya sanar da ganin watan a madadin ƴan kwamitin.
Hakan na nufin gobe Lahadi, 30 ga watan Maris na 2025 ne za a yi idin Ƙaramar Sallah na bana a faɗin Najeriya.
Sanarwar ta Najeriya ta zo ne bayan ƙasar Saudiyya ta sanar da nata ganin watan tun da yammacin yau, wato sa'o'i kaɗan kafin ganin na Najeriya.
A Jamhuriyar Nijar ma rahotanni suna nuna cewa an ga jinjirin watan na Shawwala.
No comments