Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Soyayyar Manzon Allah Ta Sa Muke Yin Zagayen Maulidi –Kalifa Aliyu Sa’idu Alti

Daga Hussaini Yero, Funtua  Shugaban darikar Tijjaniyya na yankin Funtuwa, Kalifa Aliyu Sa’idu Alti ya bayyana cewa suna Zagayen bikin murna...


Daga Hussaini Yero, Funtua 

Shugaban darikar Tijjaniyya na yankin Funtuwa, Kalifa Aliyu Sa’idu Alti ya bayyana cewa suna Zagayen bikin murnar Maulidi ne domin kara nuna soyyyarsu ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ( S A W) da aka yi duniya da lahira dominsa.

Kalifa Aliyu Sa’idu Alti ya bayyana hakan ne  a taron manema labaran da aka yi jin kadan bayan kaddamar da fara bikin zagayen Maulidin na Bana da aka yi a Zawiyyar Shek Abubakar Alti da ke kan titin Bakori cikin garin Funtuwa Jiha Katsiina.

Ya kuma bayyana cewa wannan hanyar kokarin yin zagayen garin Funtuwa da kuma yin gagarumin taro a duk shekara shekara hanyoyi ne na kara nuna wa 'yan baya soyayyar Manzon Allah ta yadda kowa zai tashi da hakan, zakaga yara a cikin gidaje har sun kosa ranar da za a yi wannan Zagayen tazo domin su sanya kaya sababbi su kuma fita zagayen gari domin suma su nuna soyayyarsu ga Manzon Allah, (S A W).

Duk da yanayin halin tsaron da ake ciki a wannan shekarar za a samu akalla yawan makarantun Islamiyyar da za su samu halartar wannan Zagayen na bana sun kai akalla dari hudu da Tamanin ( 480) duk za su halarci taron kamar yadda Kalifan ya shaidawa manem labarai.

“Mun umarci wadanda ke cikin karkara da kuma nesa da su yi hakuri saboda kare lafiya da tsaron su bisa la’akari da halin da ake ciki

Kalifan ya kuma tabbatarwa da manema labarai cewa, makasudin yin wannan zagayen garin da ake yi shi ne ana isar da sako ne na Manzon Allah (SAW)  ta hanyar yin dogaro da hadisin sa da yake cewa ku ladaftar  da 'ya'yan ku a kan abubuwa Uku wanda daga ciki akwai son Manzon Allah (S A W) kuma yawancin wadanda muke tafiya da su  wannan zagayen garin muna yi ne da daliban makarantun Islamiyyu a yau.

“Ko ni a gidana zaka ga yara idan wannan wata na tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta ya yi sai su rika kosawa ranar tazo domin su sanya sababbi kaya su nuna soyayyarsu ga Manzon Allah.

” kunga irin yadda ake farantawa yara da sababbin dinki da abinci mai dadi yaya za su ki kara son shi? domin ana faranta masu dominsa sai muka ga hakan na kara wa yaran mu son manzon Allah ( S A W) wannan ita ce isarwar sannan kuma mu nunawa duniya cewa wannan watan na rabbu’ul Auwal da aka haifi Manzon Allah (SAW) cewa ya kama kowa ya kara dagewa cikin bin Umarnin Manzon Allah ( S A W) kowa ya yi farin ciki masu abinci da dukiya kowa ya yi ta bayarwa, masu sana’ar Achaba su rage kudin Achaba masu kayan miya da dai dukkan kowa a fanninsa ya bayar da tasa gudunmawarsa domin nuna farin cikinsa da haihuwar Manzon Allah (S A W) kuma muyi amfani da wannan damar kamar yadda muka saba a yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da karuwar arziki.

” Koma wa ga Allah da kaskantar da kai a gare shi ne zai taimaka mana ta hanyar yin addu’a domin shi ne zai taimakawa jami’an tsaro, Gwamnati da dukkan komai don haka muke yin amfani da wannan dama mu yi amfani da wannan mu dub abin da Maulanmu Shaikh Dahiru Usman Bauchi ke fadi cewa fiyayyen wanda ake aikawa shi ne wanda aka aiko don haka Allah ya aiko da Annabi a(SAW) don haka mun rabe da shi muna rokon Allah ya yaye mana wannan damuwar ta rashin tsaro ya biya mana dukkan bukatun mu.

Shugaban babban kwamitin shirya taron Zagayen Maulidin Bashir Mohammad da ya samu wakilcin Barista Tijjani Ahmad, cewa anyi tsare tsaren kamar yadda aka sani illa dai kawai wani Dan canjin da aka samu sakamakon aikin gyaran hanya da ake yi a cikin garin Funtuwa .

Barista Tijjani ya ci gaba da cewa wannan zagayen da za'a yi na makarantun Islamiyuu ne kawai amma akwai zagayen da za a yi nan gaba na Sha’irai da mutanen gari baki daya, saboda haka a yau yan makantu kawai aka amince su fito wannan zagayen.

” kamar yadda aka sani ya na daga cikin ka’idojin ba a yarda a rika yin zirga zirga da abin hawa ba in dai zagaye kazo ba zaka shiga layi da mota ko Doki ko wani abu ba. Sannan sai yan canje – canjen da aka samu dalilin aikin hanya da ake yi kuma da dalili na tsaro kamar yadda aka kara gabatarwa kamar dai yadda aka sani an yi wa makarantu a kalla 480 da wani abu ban da wadanda ma sun zo lokacin yin rajistar ya wuce sai dai a ba na muna tunanin zai iya kasancewa kasa da hakan saboda umarnin da aka bayar cewa da yawa wadanda ke cikin lunguna su dakata, Kuma a cikin tsare tsaren an hana duk wata Cakuduwa tsakanon Maza da Mata na raye raye duk inda za a zo ayi raye raye tsakanin Maza da Mata an hana wanda kuma ya saba wannan ka’idar akwai hukunci mai tsauri da aka tanada a kansa da kuma maganar yin Salfi tsakanin Mace da Namiji ko yar Uwarka ce ko Matarka ce duk abin da za ku yi ku yi shi a gida idan an fito taro kawai taron ne aka fito kamar yadda Kalifa ya bayyana hidima ce ta sayidina rasulullah don haka ana son aga dabi’ar musuluncin a tare da kai kar aga sabanin hakan, aka ne a takaice game da tsare tsaren da aka yi a taron bana.

Daraktan yada labarai na zagayen gari Sayyadi Lawal Jado , godiya ya yi ga dukkan jami’an tsaro da kuma baki dayan mutanen da suka bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar yin hidimar addinin Islama saboda fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ( S A W) da fatan Allah ya saka wa kowa da alkairi ya kara wa kowa son Annabi ya kuma maida kowa gidansa lafiya Amin .

No comments