Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Ƙara Tsaro Nan Take a Katsina Bayan Zuwan Tawagar Gwamna Radda Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaro nan take a Jihar Katsina, bayan wani muhimmin taro da ya gudanar ...

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaro nan take a Jihar Katsina, bayan wani muhimmin taro da ya gudanar da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda da tawagarsa a fadar shugaban ƙasa, inda suka nemi gaggawar shiga tsakani daga gwamnatin tarayya kan matsalar tsaro da ta ta’azzara a jihar.

A yayin taron, Shugaban Ƙasa ya umurci hukumomin tsaro da su sake nazartar dabarunsu, tare da ƙara tura jiragen sintiri na sama (air drones) da kuma sauya motsin dakarun ƙasa tsakanin Katsina da iyakokin makwabta domin murƙushe ‘yan bindiga.

“Ina son ganin hukumomin tsaro sun ƙara kuzari, su sake duba dabarunsu. Idan akwai buƙatar ƙarin jiragen sama ko kuma motsa dakarun daga Katsina zuwa iyaka, su yi hakan. Kuma gobe za su kawo min rahoto,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta abu ne mai matuƙar girma, amma gwamnati ba za ta ja da baya ba.

"Mun gada matsalolin iyaka marasa tsaro, amma dole mu fuskanci wannan ƙalubale. Dakarun ƙasa suna nan, za mu ci gaba da fatattakar su,” in ji shi.

Shugaban Ƙasa ya kuma bayyana shirinsa na kafa ‘yansandan jihohi domin ƙara ƙarfin tsaro, yana mai cewa dole ne gwamnati ta kare al’umma, wuraren ibada da wuraren nishaɗi daga barazanar ta’addanci.

A nasa jawabin, Gwamna Dikko Umar Radda ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa goyon bayan da yake ba wa Katsina, inda ya ce dukkan buƙatun da suka gabatar tun da farko suna samun amincewa.

“Shugaban Ƙasa ya tabbatar da kansa a matsayin ɗan Katsina. Muna godiya ƙwarai bisa damuwar da yake nuna mana,” in ji shi.

Shi ma Sarkin Katsina, wanda Waziri na Katsina, Sanata Ibrahim Ida ya wakilta, ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro tare da kafa bataliya ta soja da rundunar MOPOL a Kudancin Katsina.

Ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan 40 wajen tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aiki duk da ƙarancin kuɗi, inda ya roƙi gwamnatin tarayya ta tallafa da kudaden biyan diyya da kuma taimakon waɗanda abin ya rutsa da su.

Wannan zama dai na ƙara tabbatar da kokarin gwamnati wajen kawo ƙarshen ta’addancin ‘yan bindiga da ke addabar jihar Katsina da sauran sassan Arewa maso Yamma.

No comments