Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Jami’ar Greenfield dake jihar Kaduna a daren ranar Talata, inda suka ka...
Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Jami’ar Greenfield dake jihar Kaduna a daren ranar Talata, inda suka kashe mutum daya da awon gaba da dalibai da dama.
Ita dai Jami’ar Greenfield jami’a ce mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba, wacce ta fara aiki shekaru uku da suka gabata, kuma mazauninta na kan titin Kaduna zuwa Abuja.
Majiyarmu ta Jarirdar DESERT HERALD ta labarto cewa; wanda ya assasa jami’ar ya tabbatar musu cewa; tabbas an kai hari Jami’ar, kuma ‘yan bindiga sun sace dalibai da dama. Wanda ya ce ya zuwa yanzu ba su tabbatar da adadin daliban da aka sace ba. Amma majiyar tamu ta ce ‘yan bindigar sun kashe ma’aikacin Jami’ar daya a yayin da suka kai harin.
Majiyarmu Ta Zayyano Sunyen Dalibai maza da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su:
1. Abraham Akinje
2. Fortune Alhassan
3. Miracle John
4. Miracle Turman
5. Jesse Jakiri
6. Joseph Davies
7. Abdullahi Yusuf
8. John Yari
9. Micheal Samson Ladan
10. Abdulkareem Ibrahim
11. Kabir Hamisu
12. Lemuel Adamu
13. Isreal Antonio
14. Isreal Musa
15. Nelson David
16. Mariam Nalado
17. Abdulkadir Abubakar
No comments