Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Jami'ar Greenfield Sun Nemi Naira Miliyan 800

Daya daga cikin iyalan daliban Jami'ar Greenfield da ke Kaduna ya ce yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 800 matsay...


Daya daga cikin iyalan daliban Jami'ar Greenfield da ke Kaduna ya ce yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sako daliban 23, kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ana tattaunawa, masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan daliban suna neman a biya Naira miliyan 800," a cewar, Georgina Stephen, yar uwan daya daga cikin daliban da aka ace.

Ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci 'yan gidansu su biya Naira miliyan 8 kudin fansa kafin su sako 'yan'uwanta da ke tsare a hannunsu.

A cewar Georgina, daliban 23 da aka sace sun kumshi mata 14 da kuma maza 6 da kuma ma'aikatan jami'ar.

Ta ce masu garkuwa da mutanen suna azabtar da daliban inda suka ce idan ba a biyan kudin ba, za su halaka dukkan daliban da suka sace.

No comments