Daga Muhammad Farouk Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya yi zargin cewa ana yunkurin sakin wani bidiyo ...
Daga Muhammad Farouk
Ministan sadarwa da tattalin arzikin
zamani, Isa Ali Pantami, ya yi zargin cewa ana yunkurin sakin wani bidiyo da
aka kirkira domin a bata masa suna.
Ministan sadarwar ya bayyana hakan
ne ta bakin Kakakinsa, Uwa Suleiman, inda ya ce ba zai yadda mutuncinsa da ya
dade yana ginawa a bata masa ba.
“mun samu bayanan sirri masu karfi da ke nuni
da cewa wadansu kusoshi da suke kashe makudan kudade wajen daukar nauyin kamfen
din bata sunan ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Ibrahim
Pantami, sun shirya tsaf domin daukar mataki na gaba akan shirin na su”, inji
Uwa Suleiman.
Ministan ya ci gaba da cewa; “a
wannan lokacin, wadannan kusoshin marasa mutunci sun hada hannu da wadanda suke
hulda da su kamar yadda suka ba, inda za su saki wani bidiyo da suka kirkira da
zai nuna ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali a wani irin
yanayi da zai bata masa suna”, inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; “mun yi
mamaki bisa wannan yunkurin na su wanda yake nuna yadda suka zaku duk da nakasu
da faduwa da suka rika samu akan ministan a yunkurinsu na baya”, ta lurantar.
“bayan sun kirkiri karya da gaskiya suna
alakanta ministan da ta’addanci, duk da hujjojinsa na yakar kungiyar ta’addanci
na Boko Haram, wadannan mamuguntan ba su tsaya nan ba, sun tashi haikan wajen
kirkirar takardar boge da ka iya haifar da tashin hankali a kasarnan. Wanda shima
cikin ikon Allah da taimakon ‘yan Nijeriya masu son zaman lafiya, shima shirin
na su ya fadi warwas”, ta tabbatar.
Uwa
Suleiman ta karkare da cewa; “wannan sanarwar domin shelantawa al’umma shirin
su da suke kokarin yi ne tare da gargadin wadanda suke hakan akan abin da ka
iya biyo baya idan suka aikata hakan. Mai girma ministan ba zai zauna haka nan
ya rika ganin mutuncinsa da ya dade yana ginawa a matsayinsa na shugaban al’umma,
Malamin addinin musulunci, kuma ma’aikacin gwamnati wadansu da ake biya na bata
shi da yi masa cin kasa ba tare da gaskiya ko tsoron Allah ba”, ta tabbatar.
No comments