Daga Auwal Adam Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya bayyana cewa akalla kauyaku 50 ne a kananan hukumomi biyar na jihar ta Neja...
Daga Auwal Adam
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja
ya bayyana cewa akalla kauyaku 50 ne a kananan hukumomi biyar na jihar ta Neja
suka fada hannun ‘yan bindiga.
Gwamnan ya ce wadannan kauyukan
yanzu babu kowa sakamakon hare-haren ‘yan bindigar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar
Litinin a garin Minna a yayin da yake bude taron horaswa na kwana biyu wanda
aka shiryawa Daraktocin kananan hukumomi da kuma jami’an karbar haraji.
An shirya taron ne domin bunkasa
hanyoyin tara kudaden shiga daga kananan hukumomi na jihar Neja.
Hukumar lura da kananan hukumomi na
jihar ne ya shirya taron domin fito da hanyoyin tara kudaden haraji domin
bunkasa ci gaban jihar da magance matsalolin da ake fuskanta da ya hada na
matsalar tsaro da kuma kwararar ‘yan gudun hijira.
Gwamnan ya ce; “a yanzu haka akwai ‘yan
gudun hijira dubu uku da suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijirar a Minna, baya
ga wadanda muke da su a sauran kananan hukumomin. A ina zamu samu kudaden da
zamu lura da su?” ya tambaya.
Ya ci gaba da cewa; “akwai bukatar
mu rage kudaden da muke kashewa, mu hada hannu domin ganin yadda zamu magance
matsalar ma’aikatan boge da kuma masu sace kudaden jihar”, ya lurantar.
Ya yi gargadin cewa; gwamnati ba za
ta ji kyashin korar wadanda ba sa kawo wani ci gaba ga tsarinta ba.
Gwamna Bello ya ce taron ya zo ne a
daidai lokacin da kasar da kuma sauran kasashe ke fuskantar matsalar tattalin arziki
sakamakon matsalar tsaro da kuma annobar korona ba.
No comments