Daga Muhammad Farouk Umma Abdullahi Getso, tsohuwar 'yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a jam'iyyar YPP a zaben 2019, t...
Daga Muhammad Farouk
Umma Abdullahi Getso, tsohuwar 'yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a jam'iyyar YPP a zaben 2019, ta nuna takaicinta na yadda dan Nijeriya ke sakaka yana mika wuya ga zaluncin da ake masa ba.
Umma Getso ta bayyana hakan ne a yayin da gidan Talabijin na LIBERTY ke tattaunawa da ita kan halin da Nijeriya ta fada. MADOGARA ta labarto Umma Abdullahi Getso na cewa; "mutanen da ke juya Nijeriya a kirge suke. Ban taba ganin mutumin da yake mika wuya ga zalunci irin dan Nijeriya ba. An zalunceka yau, gobe ka kuma dawowa, an kuma zaluntarka gobe", inji ta.
Har wala yau a wani bangare na jawabinta ta ci gaba da cewa; "kuma wadannan shugabanni da kake fadi, shugabannin duka namu ba sune suke jujjuyawa ba? Tun 1960s, ’ya’yansu da ‘ya’yan da suka raina, sune suka zo kuma yanzu suka zame mana shuwagabanni na farar hula", ta tabbatar.
Da take amsa tambaya akan shin ba ta ganin talakawa na iya bakin kokarinsu wajen zabo shugabannin da ya kamata, sai ta ka da baki ta ce; “a’a. abin da yake yi akwai mai ban mamaki. Yanzu idan ka duba zaben 2019, akwai mutane kwararru da suka fito a fanni-fanni a kowanne mataki, haka ne ko ba haka ba? Akwai wani abu guda daya, ina zargin kullum su kansu masu zaben al’ummar Nijeriya. Na biyu; ina zargin ‘yan jaridu ina ganin laifukansu. Saboda? Nijeriya ta zama wata kasa, magana ce ta; mene ne a hannunka? Me zaka iya bayarwa? Idan aka dauko wane aka ce mutumin kirki ne, wane na da hali kaza, wane ya iya kaza, wane yana kaza, sai ka ji an ce a wacce jam’iyya yake?”, ta karkare.
No comments