Rahotanni daga garin Geidam ta jihar Yobe na nuni da cewa; har ya zuwa tsakiyar ranar yau Asabar mayakan Boko Haram na cikin gar...
Rahotanni daga garin Geidam ta jihar Yobe na nuni da cewa; har ya zuwa tsakiyar ranar yau Asabar mayakan Boko Haram na cikin garin Geidam dake Jihar Yobe bayan harin da suka kai yammacin jiya Juma’a da misalin karfe 5:30pm kamar yadda gidan Rediyon Faransa, RFI Hausa ya labarto.
Wani mazaunin garin kuma shaidar gani da ido ya ce har ya zuwa yau da rana mayakan na cikin garin dauke da makamai da kuma sabbin motocin yaki da suka yi amfani da su wajen farma garin.
Mutumin ya kara da cewa mayakan sun kai hari yau da safe wajen cinna wuta a wasu gine-gine da kuma fasa shaguna suna kwashe abinci, yayin da akasarin mutanen garin suka nemi mafaka a cikin gidajen su, wasu kuma suka fara sulalewa ta hanyar daji suna barin garin.
Wata motar aiki da Boko Haram din suka bankawa wuta.
Shaidar gani da ido ya ce ya zuwa yau da safe sun bar mutane sun fara fita amma daga bisani sun fara daukar mataki akan su, sai dai ya ce shi bai ga ko da mutum guda da aka kashe a inda yake ba.
MUNA CIKIN TASHIN HANKALI
Mutumin ya ce mayakan sun rarraba wasika ga mutanen garin amma shi bai samu kwanciyar hankalin da zai iya karanta ba a lokacin da muka tattauna da shi.
Shaidar gani da idon ya ce; a jiya jirgin soji ya kai hari kuma ya kashe mutane 11, yayin da aka ce kuma sun yi musayar wuta da sojoji lokacin da suka je fasa shaguna domin dibar abinci.
Mutumin ya ce akasarin maharan matasa ne masu kananan shekaru kuma suna dauke da muggan makamai.
Wani shaida na biyu da muka zanta da shi wanda ke kan hanyarsa da fita daga garin ya ce duk da sojoji na kokari amma ba su da kwanciyar hankali ganin yadda mayakan suka ci gaba da cin karensu babu babbaka a garin.
Tuni dai kakakin 'Yan sandan Jihar Yobe Dungus Abdulkarim ya tabbatar da kai wannan hari.
No comments