Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Bala Ya Raba Motocin Sintiri 50 Ga Jami'an Tsaro

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kaddamar da raba motocin sintiri ga jami'an tsaro a wani matakin ing...


Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kaddamar da raba motocin sintiri ga jami'an tsaro a wani matakin inganta zaman lafiya da ingantuwar tsaron rayuka da dukiyar al'umar jihar Bauchi. 


Lawal Muazu Bauchi, mai tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani ya labarto cewa; da yake jawabi yayin bikin rabon, Gwamna Bala Muhammad ya ce kalubalen da jami'an tsaro ke fama da su sun hada da Karancin motocin sintiri a saboda haka shirin zai taimaka wajen yaki da fashi da makami, ta'addanci da sauran ayyukan bata-gari.

Ya yabawa jami'an tsaron kan marawa gwamnatinsa baya wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar Bauchi kana ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ladabtar da masu aikata laifuka ta hanyar damke su tare da gurfanar da su gaban kuliya. 

Gwamna Bala ya ce tsaron rayuka da dukiyar al'uma nauyi ne da ya rataya akan gwamnati amma hakan ba zai samu ba sai al'umar jiha da Kasa sun mara mata baya ta hanyar bada rahoton bata-gari ga jami'an tsaro. 

Gwamnan ya yi amfani da damar wajen yabawa kungiyoyin 'Yan banga kan ayyukan sanya ido da inganta tsaro inda yace gwamnatinsa ta gamsu da kyakkyawuyar alakar dake tsakanin Yan sanda da kwamitocin tsaro na unguwanni. 

Har wa yau gwamnan ya yi amfani da damar wajen yabawa al'ummar jiha kan goyon baya da hadin kai da suke bada jami'an tsaro kana ya yi fatan darewar hakan. 

Rabon motocin ya gudana kamar haka; 

1. Shadawanka Artillery Brigade -04

2. Sojin sama -01 

3. Rundunar Yan sanda - 16

4. Jami'an kula da kiyaye hadura - 02

5. Jami'an tsaron Civil Defence -02

6. Hukumar BAROTA -04

7. Jami'an tsaron farin kaya -02

8. Hisbah -01

9. Yan banga -01

10. Danga Security -01

11. Kungiyar maharba -04

12. Ofishin me tallafawa gwamna kan sintirin hanyoyin -01

13. Asibitin kwararru - 01

14. Hukumar da'a  ta jiha -01

15. Ma'aikatar filaye da safiyo- 01

16. Hukumar kula da inganta birane ta jiha-01

17.  Ofishin hulda na Birnin Tarayya-01

18. Kwamitin yaKi da cin zarafin mata da yara-01

19. Ajiyayyu motoci - 03

A Madadin shugaban 'yan sanda na kasa,  Mista Johnson Babatunde wanda ya yi jawabin godiya a madadin jami'an tsaron, ya yabawa Gwamna Bala Muhammad bisa rabon.

No comments