Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Buhari Ya Yi Kakkausan Suka Ga 'Yan Bindigar Da Suka Kashe Daliban Jami'a A Kaduna

Daga Muhammad Farouk A ranar Asabar shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da Allah-wadai da kashe dalibai uku na Jami'ar Greenf...

Daga Muhammad Farouk

A ranar Asabar shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da Allah-wadai da kashe dalibai uku na Jami'ar Greenfield ta Jihar Kaduna da 'yan bindiga suka sace. 

Shugaba Buhari ya bayyana daliban a matsayin matasa masu kwazo wanda batagari suka kawo karshen rayuwarsu suna ganiyarsu. 

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a sanarwar da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar ya kuma sanya hannu, inda ya ce shugaba Buhari ya ce; "ina taya iyalai alhinin wannan rashi da aka yi. Allah yasa ruhinsu ya kasance cikin salama", inji shugaban. 


Da yake magana a kan garkuwa da jama'a da kashe-kashe da ake ci gaba da yi a Kaduna, shugaban kasa ya ce ba abin a yarda bane, inda ya bayyana hare-haren a matsayin na "ta'addanci", tare da zargin wasu daga cikin shugabannin siyasa da na addini da rura wutar kiyayya a yayin da iyalai ke jimamin wannan ta'addancin da aka yi musu. "fuskantar wannan lamari yana bukatar tausayawa tare da hadin hannu a matsayin al'umma daya domin fuskantar wadannan bata garin da suke haifar da barazana ga Dimokuradiyyarmu da zaman lafiyar kasarnan", Inji shi. 

Ya bada tabbacin cewa wadanda suke ganin za su iya samun riba daga kudaden fansa da ake biya ko a siyasa; "za su fahimci nan bada jimawa ba za su fada irin barazanar da suka jefa wasu ciki", ya tabbatar. 

Ya karkare da cewa da da magana cikin kakkausan suka, inda ya ce; "kashe-kasheda ake yi daga 'yan bindiga, garkuwa da jama'a da kuma siyasar kashe-kashe abu ne da zan murkushe shi da dukkanin arzikin da muke da shi", ya tabbatar. 

No comments