Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

EFCC Ta Garkame Tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

  Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, EFCC na ci gaba da yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tambayoyi kan wa...

 


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, EFCC na ci gaba da yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tambayoyi kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa.

An tattaro cewa an rike tsohon gwamnan a ofishin hukumar na Sakkwato na tsawon awanni takwas har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton a ranar Talata, 20 ga watan Afrilu.

Majiya ta ce an bayar da belin Yari amma bai iya cika sharuddan belin ba kamar yadda Jaridar Premium Times ta labarto.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yana hannun hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

 


No comments