Gamayyar Kungiyoyi fararen hula masu kare hakki, CSOs sun yi kira da Shugaba Buhari da ya yi watsi da masu neman a sauke Dr Isa Ali Pa...
Gamayyar Kungiyoyi fararen hula masu kare hakki, CSOs sun yi kira da Shugaba Buhari da ya yi watsi da masu neman a sauke Dr Isa Ali Pantami , domin a cewar kungiyoyin, wasu marasa kishin kasa ne da ba su son zaman lafiya da tsaro suka dauki nauyin abin saboda a dakatar da rijistar lamabar zama dan kasa wato NIN.
Kungiyoyin sun ce Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani mutum
ne mai nagarta da ke kawo sauye-sauye masu amfani a kasar.
Gamayyar kungiyoyin kare
hakkin bil'adama da tabbatar da mulki na gari ta ce wasu ne suka dauki nauyin
kiraye-kirayen da ake yi a kafafen sada zumunta na neman sauke ministan Sadarwa
da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami da nufin kara lalata harkar tsaro a
kasar.
Hadakar ta ce wadanda suka dauki nauyin abin suna ci gaba da samun
riba daga kalubalen rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassar kasar, kamar
yadda Daily Trust ta ruwaito.
A jawabin da ya yi a Legas a ranar Talata 20 ga watan Afrilu,
jagoran hadakar, Kwamared Declan Ihekaire, ya ce sun damu kan ganin yadda ake
ci ci gaba da neman sai Pantami ya sauka.
Gamayyar ta bayyana Pantami a matsayin mutum mai nagarta da basira
kuma daga cikin mutane masu muhimmanci a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ihekaire ya ce tilas ta sa suka fito domin yin Allah wadai da bata
sunan da wasu marasa kishin kasa da ke amfana da rashin tsaro ke yi wa Dr
Pantami da masu adawa da batun rajistan NIN wanda zai taimakawa kasar wurin
dakile laifuka da samar da tsaro.
Har wala yau, kungiyoyin sun ce sun gamsu da gaskiya irin ta Dr Isa
Pantami inda ya amsa cewa a baya ya furta wasu maganganu da ake yi wa kallon
goyon bayan kungiyoyin ta'addanci amma tuni girma ya zo masa kuma ya sauya
tunaninsa. Don haka kungiyar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi
da masu kiraye-kirayen ya sauke Dr Pantami kuma kada ya bari marasa kishin kasa
su lalata masa gwamnati.
No comments