Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki kasashen duniya da zu taimaka wa Nijeriya da kasashen kudu da sahara wajen magance mats...
Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya roki kasashen duniya da zu taimaka wa Nijeriya da kasashen
kudu da sahara wajen magance matsalar tsaro domin hana yaduwarta.
Shugaba Buhari ya nemi agajin hakan ne
a wani taron tattaunawa da ya yi da Sakatarten Harkokin Wajen Amurka, Mr.
Anthony Blinken ta intanet.
Shugaba Buhari ya bukaci Amurka da
ta yi nazari kan maido da rundunar AFRICOM daga Jamus zuwa nahiyar Afrika domin
karfafa matakan magance matsalar tsaro a nahiyar.
“Kalubalen tsaro dai a Nijeriya na
ci gaba da zama abin damuwa a gare mu wanda kuma ke mana mummunan tasiri ganin halin matsiln lambar da ake fuskanta a Sahel da Tsakiyar Afrika da
kuma Yammacin Afrika har ma da yankin Tafkin Chadi” inji Shugaba Buhari.
Shugaban ya kara da cewa, Nijeriya
za ta inganta alakarta da aminanta domin aiki tare wajen samar da tsaro
ga kowa.
Nijjeriya na cikin kasashen Afrika da
ke fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram baya ga matsalar 'yan bindiga da
ke kisa babu kakkautawa tare da sace jama'a domin karbar kudin fansa.
No comments