Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Raunata Malamai Da Dalibai Saboda Hukunta Yaron Wata Mata Da Aka Yi

Daga Muhammad Farouk Akalla Malamai biyar da dalibai biyu ne na makarantar Sakandaren Gwamnati dake Kufang a karamar Hukumar Jos...


Daga Muhammad Farouk

Akalla Malamai biyar da dalibai biyu ne na makarantar Sakandaren Gwamnati dake Kufang a karamar Hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato sojin Nijeriya suka raunata kamar yadda MADOGARA ta labarto. 

Sojojin sun dira makarantar ne bisa jagorancin wata mata biyon bayan hukunta danta wanda dalibi ne a makarantar wanda wani Malami ya yi. 

Majiyarmu ta MK-Reporters ta labarto cewa; Sojoji uku ne suka dira makarantar cikin Khakinsu na Soja a cikin motar sojoji mai lambar DHQ370 da misalin karfe 8:45 na safe. 

Sojojin a cewar ma'aikaci a makarantar, Mr Nanzing Lamtur ya ce daga zuwansu suka fito da wani Malami daga ofishinsa na mataimakin shugaban sashe, inda suka yi masa dukan kawo wuka ba tare da wani dalili ba. Sai dai shugaban sashen, Mr. Mauka Solomon wanda ake zargin shi ya hukunta dan na ta ne shi ne wanda suka zo nema. 

Mauka Solomon shi ma sojojin sun raunata shi,  sai dai ba farko lokacin da sojojin suka isa makarantar ya fita daga ofishinsa, amma rahotanni sun tabbatar da cewa daga baya ya dawo bayan da ya jiwo makarantar ta rude; "isowarsa ke sa wuya matarnan ta nuna shi inda suka bar Malamin farko da suka fara duka bayan sun raunata masa idonsa da wani bangare na jikinsa suka koma kansa. Sun yi shugaban sashen lilis, suka kuma jefa shi mota da nufin za su tafi da shi", inji Lamtur. 
    Mauka Solomon da sojoji suka raunata. 

Lamtur ya ci gaba da cewa; sai shi (Lamtur) da wadansu Malamai suka yi yunkurin jin me ke faruwa domin su ceci abokan aikinsu, sai suma sojojin suka shiga bugunsu. Har wala yau bayanai sun nuna cewa sojojin sun raunata dalibai biyu- Daniel Chukwuka da Wakzing Puslong a kunne da hannunsu. Inda sauran daliban kuwa suka yi maza suka kulle makarantar bayan Malamai sun yi kiran dauki. 

     Dalibai biyu da sojojin suka raunata

Bayanai sun nuna cewa; jim kadan sai ga tawagar sojoji da 'yan sanda sun isa makarantar a daidai lokacin da wadancan sojoji uku ke kokarin gudu da shugaban sashe na makarantar. "Nan take aka kama su aka tafi da su, a yayin da kuma Malamai da dalibai da aka raunata aka wuce da su asibiti", inji majiyarmu. 

Bayanai sun nuna cewa; matar da ta zo da sojojin ta tabbatar da cewa wani oganta ne wanda yake ritaya Janar ne a Jos ya hada ta da sojojin. "Akwai yiwuwar za a gurfanar da ita a gaban kotu", Inji majiyarmu. 

      Motar da sojoji ukun suka zo da ita. 

Tuni aka kulle makarantar saboda fargabar ballewar rashin tsaro. Har ya zuwa hada rahoton nan, majiyarmu ta yi yunkurin jin ta bakin 'yan sanda da soja amma abin ya ci tura, sai dai majiyarmu ta ce an rufe makarantar saboda tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo a daidai wannan lokacin.

      An rufe makarantar saboda firgici

"Gaskiya ba ma cikin kwanciyar hankali. Rayuwarmu na cikin barazana, ba za mu iya sakewa yanzu mu yi karatu ba a makarantar. Duka dalibai da Malaman suna cikin barazana", Inji Lami Aminu daya daga cikin dalibai na makarantar. 

No comments