Gidan Rediyon Jamus na DW Hausa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa; rahotannin da ke shigo mana da dumi-dumi sun nuna cewa ...
Gidan Rediyon Jamus na DW Hausa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa; rahotannin da ke shigo mana da dumi-dumi sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun karbe iko da garin Gaidam a jihar Yoben Nijeriya bayan wani hari da su ka kai tun ranar Juma’a da yamma.
Wasu mutanen garin sun tabbatarwa da DW cewa cewa tun a ranar Juma‘a mayakan suka shiga garin kuma suka kwana a ciki, inda suka rarraba wasu takardu da ke neman jama'a su hada kai da Daularsu.
Ya zuwa yanzu babu cikakken karin bayani.
Ga kwafin takardar da suka raba;
No comments