Kamfanin sadarwa na MTN ya ce kwastomominsa a Nijeriya ba za su iya sayan 'Data' kan wayoyinsu ba daga karfe 12 na dar...
Kamfanin sadarwa na MTN ya ce kwastomominsa a Nijeriya ba za su iya sayan 'Data' kan wayoyinsu ba daga karfe 12 na daren yau Juma'a (Asabar) zuwa karfe shida na safiyar ranar Lahadi.
MTN sun bayyana hakan n a cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a daren yau Juma'a mai taken, 'Service Upgrade Notice' a shafinsa na sada zumunta.
MTN sun aika da sako da cewa; “saboda bunkasawa, ba za a sami sayan Data ba daga 12 na tsakar daren yau zuwa 6 na safe a ranar 25 ga Afrilun 2021", inji su.
Sun kara da cewa; “idan kuna da bukatar DATA, da fatan za ku yi caji a yau sannan ku sayi Data din. Muna neman gafara saboda rashin jin daÉ—in hakan", suka lurantar.
Ga sanarwar da MTN suka wallafa;
No comments