Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

APC Ta Sanya Wa Jonathan Ka’idodi Kafin Su Ba Shi Takara A 2023

  Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce za ta iya bai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan damar tsayawa takarar shugaban kasa a...

 


Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce za ta iya bai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan damar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 idan ya shigar jam'iyyar. Ya ce komawar jonathan APC zai zama babban abun alfahari a gare su.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa John Akpanudoedehe, sakataren kwamitin riko na jam’iyyar APCn na bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels.

Ya ce za a ba Jonathan damar yin takarar kujerar shugaban kasa a 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar, kamar kowane mutum mai sha’awar tsayawa takara.

“Za mu yi masa maraba; hakan kuma zai karfafa jam’iyyar, ”in ji Akpanudoedehe.


No comments