Daga El-Zaharadeen Umar Shahararren mawakin siyasar nan na ƙasar Hausa kuma mawakin shugaba Buhari Dauda Abdullahi Kahutu Rarara...
Daga El-Zaharadeen Umar
Shahararren mawakin siyasar nan na ƙasar Hausa kuma mawakin shugaba Buhari Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya gargaɗi shugaban ƙasa Buhari da kadda ya sake ya yaki Bola Ahmad Tinubu saboda ya taimaki shi a lokacin da yake buƙatar taimako.
Rarara ya bayyana haka acikin wani faifon bidiyo da ya saki dangane da batun da wasu 'ya 'yan jam'iyyar APC ke cewa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa shugaban ƙasa Buhari gorin taimako.
Wannan magana da Bola ya yi ga alama bata yi wa wasu daga cikin magoya bayan shugaba Buhari daɗi ba, saboda suna ganin babu wani dalili da zai sa Bola Ahmad Tinubu ya share wuri yana maganganu masu kama da soka ta kai tsaye ga shugaba Buhari
Inda har suke ganin kamar Bola Ahmad Tinubu yana ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa, saboda neman mulki har yana ƙoƙarin cin fuskar shugaban ƙasa Muhammad Buhari.
Mawakin wanda ya ce Bola Ahmad Tinubu ya taimaki shugaban ƙasa Muhammad Buhari kuma ko shi Buhari bai isa ya ƙaryata hakan ba, ya ce har na kusa da Buharin ma sun san haka.
Haka hatta ita kanta uwar jam'iyya ta yi barazanar ɗaukar matakin ladaftarwa ga Bola Ahmad Tinubu idan har bai janye waɗancan kalamai na shi ba.
An ruwaito shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu yana cewa za su iya ɗaukar mataki akan Bola Tinubu dangane da wadancan kalamai na shi.
Shi kuwa mawakin na Buhari Dauda Kahutu Rarara ya ce wasu da ke ɗaukar wannan magana da zafi da yawan su 'yan 'good evening ne' wato dai 'yan ta more ne, amma ba su san da wancan zancen ba.
" An samu wani lokaci da Buhari ke buƙatar taimako kuma akwai 'yan arewa da suke da halin da za su taimaka masa amma suka ƙi taimakonsa sai shi Bola Tinubu ɗin ya taimaki Buhari kuma ya samu abinda yake so inda har ya kawo yanzu" in ji shi.
Saboda haka a cewar Rarara babu wanda ya isa ya ce Bola Tinubu bai taimaki Buhari ba kuma shi Buharin ya sani, ya ce hatta mu ɗin nan mun sani.
Ya kara da cewa shi Bola Tinubu abokin siyasar Buhari ne, ya taimaki Buhari ya zama ɗan takara kuma yai zo ya taimaka aka kafa gwamnati da shi.
Sannan duk wanda ka ji yana wata magana bai da san wancan taimakon ba, mafiyawansu cewa aka yi kai kawo ɗan ka ko ƙaninka ko ɗan uwanks a bashi muƙami saboda ba za su san da wancan taimakon ba. In ji Rarara.
A cewar Rarara baban abinda zai yi na nunawa arewa dattako shi ne, ko dai ya goyi bayan Tinubu ko kuma ya bada dama ga kowa da kowa ya shiga zaɓen fidda gwani wanda Allah ya ba shikenan.
Ya ƙara da cewa duk da an san irin gudunmawar da Bola Ahmad Tinubu ya ba Buhari ya har zama shugaban ƙasa bai zama dole sai Buhari ya yi masa haka ba, amma dai idan ya yi masa to ya maida biki.
No comments