An rantsar da Dakta Dikko Umar Radda na jam'iyyar APC a matsayin sabon gwamnan jihar Katsina a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cik...
An rantsar da Dakta Dikko Umar Radda na jam'iyyar APC a matsayin sabon gwamnan jihar Katsina a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cikin garin Katsina.
Babban alkalin jihar Danladi Abubakar shi ne ya rantsar da gwamnan tare da mataimakinsa Faruk Jobe, a bikin da mai barin-gado Aminu Bello Masari da mataimakinsa Muntari Lawal da sauran manyan baki suka halarta.
Daga cikin manyan bakin akwai gwamnan jihar Maradi ta Nijar, Abubakar Shuaibu, da tsohon gwamnan jihar ta Katsina Ibrahim Shehu Shema, da kuma tsohon gwamnan Kaduna Abba Musa Rimi.
Sabon gwamnan na Kaduna shi ne tsohon shugaban hukumar bunkasa kananan da matsakaitan sana'o'i ta Najeriya, SMEDAN.
Sannan ya kasance tsohon shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Masari, kuma ya shugabanci karamar hukumar Charanchi a jihar ta katsina.
No comments