Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dauda Lawal Ya Zama Sabon Gwamna a Zamfara

  Dauda Lawal ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara bayan ya sha rantsuwar kama aiki a Gusau babban birnin jihar. Ya karbi mulki daga wurin ts...

 


Dauda Lawal ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara bayan ya sha rantsuwar kama aiki a Gusau babban birnin jihar.

Ya karbi mulki daga wurin tsohon gwamnan jihar Bello Mohammed Matawalle.

An yi bikin ne a filin baje koli da ke Gusau, a birnin jihar Zamfara.

Shi ma mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mallam Mani Muni ya sha rantsuwa.

Sabon gwamnan zai soma aiki ne a yayin da jihar ke fama da matsalar tsaro ta 'yan bindiga wadanda ke kashe mutane tare da sace wadansu domin karbar kudin fansha.

No comments