Gwaman jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya, ya dakatar da karbar duk wani haraji daga direbobin motoci da da kuma babura masu kaf...
Gwaman jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya, ya dakatar da karbar duk wani haraji daga direbobin motoci da da kuma babura masu kafa uku na haya a jihar.
Umarnin yana kunshe ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce umarnin na daga cikin alkawarin da gwamnan ya yi ne a lokacin yakin neman zabe na gyara tsrain karbar haraji a jihar, domin kawo karshen yadda ake muzgunawa da kuma tatsar masu motoci kudade.
Umarnin ya shafi dukkanin wani haraji da ake karba da sunan gwamnatin jiha daga masu motocin da sauran abubuwan sufuri da ke jihar.
Gwamnatin ta ce tsarin da ake amfani da shi wajen karbar harajin tsohon yayi ne wanda kuma yake cutar da rayuwar al'umma da tattalin arzikin jihar, saboda haka ta ce a dakatar da shi har sai ta sake nazari.
No comments