Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Mista Dele Alake a matsayin mai magana da yawunsa sa’o’i kadan bayan rantsar da shi a ra...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Mista Dele Alake a matsayin mai magana da yawunsa sa’o’i kadan bayan rantsar da shi a ranar Litinin.
Mista Alake ya dade da zama abokin huldar Tinubu. Ya rike mukamin kwamishinan yada labarai da dabaru daga 1999 zuwa 2007 a lokacin yana gwamnan jihar Legas.
Haka zalika kuma shugaban ya nada Ambasada Kunle Adeleke a matsayin shugaban bin ka’ida (SCOP) ga shugaban kasa.
An nada shugaban matasan APC na kasa Olusegun Dada a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai na zamani.
Mukaman sun soma aiki nan take.
No comments