Daga Hussain Ibrahim A yau Litinin aka rantsar da sabon gwamnan jihar Zamfara, a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal...
Daga Hussain Ibrahim
A yau Litinin aka rantsar da sabon gwamnan jihar Zamfara, a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal Dare, Mai sharia Kulu Aliyu ce ta rantsar da shi.
A jawabinsa ya yi alkawarin bayar da muhimmanci kan matsalar tsaro, noma, samar da ayyukan yi da samar da ababen more rayuwa domin ci gaban jihar.
A cewarsa, rashin aikin yi ga matasa ya ta'azzara matsalar tsaro a jihar Zamfara, a don haka akwai bukatar gwamnatinsa za ta hada kai da gwamnatin tarayya domin ceto jihar domin a samu zaman lafiya.
"Kuma da yardar Allah zamu shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar, domin dawo da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar", inji shi.
Dakta Dauda ya ci gaba da nuna cewa gwamnatinsa za ta ba da muhimmanci sosai a fannin noma da samar da ayyukan yi domin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin jihar.
"Gwamnatina za ta hada hannu da hukumomin bayar da tallafi da masu zuba jari na kasashen waje domin bunkasa jihar ta fuskar samar da ababen more rayuwa da ci gaban al’umma duba da yadda jihar Zamfara aka bar ta baya wajen rashin isassun hanyoyin samun kudin shiga domin bunkasa jihar”.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bai wa gwamnatinsa duk goyan bayan da shawarwari domin cimma manufofin gwamnatinsa.
"Ina so in yi kira ga daukacin al'ummar jihar Zamfara cewa Zamfara ba ta da kwanciyar hankali kuma za mu yi duk mai yiwuwa donin ceto jihar daga halin da take ciki", a jawabin sabon gwamna Dauda Lawal Dare.
No comments