Daga Abdullahi Idris, Bauchi An gudanar da bikin rantsar da gwamna Bala na jihar Bauchi da mataimakinsa Hon. Auwal Jatau bayan ...
Daga Abdullahi Idris, Bauchi
An gudanar da bikin rantsar da gwamna Bala na jihar Bauchi da mataimakinsa Hon. Auwal Jatau bayan samun nasarar lashe zaben Karo na biyu a karkashin tutar Jam’iyyar PDP.
An gudanar da wannan bikin ne a harabar wasanni na Abubakar Tafawa Balewa dake Birnin Bauchin Yakubu.
Babban Alkalin Alkalai ta jihar Bauchi, mai shari'a Rabi Talatu Umar, ita ce ta rantsar da gwamna da mataimakinsa domin kama aiki da misali karfe 12:53 pm na rana a yau Litinin.
Kafin rantsar da gwamnan, ya karbi faretin bangirma daga jami’an ‘yan sandan Nijeriya, wanda a wajen rantsar da gwamnan ya samu halartar Sarakuna, 'yan siyasa, masu fatan alheri da sauran magoya bayan jam’iyyar PDP.
A wajen rantsuwar ta su, gwamnan da mataimakinsa an karanto tarihinsu, da gwagwarmayar siyasarsu da mukamai da suka rike a rayuwa har zuwa yau Litinin.
No comments