Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cikin Shekaru Biyu Jami'an Tsaron Nijeriya Kusan 1000 Aka Kashe - Bincike

Daga Muhammad Farouk  Akalla sojojin Nijeriya da ‘yan sanda 965 ne suka mutu a bakin aikinsu, cikin shekaru biyu sakamakon karuw...


Daga Muhammad Farouk 

Akalla sojojin Nijeriya da ‘yan sanda 965 ne suka mutu a bakin aikinsu, cikin shekaru biyu sakamakon karuwar hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai irinsu Boko Haram, da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma ayyukan masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB da sauran kawayensu.

Jaridar Daily Trust ta bi diddigin rahotannin hare-hare daban-daban da suka shafi kashe jami'an 'yan sanda da sojoji tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Afrilu 2023, inda sakamakon binciken ya nuna jami'an tsaron Nijeriya na rasa rayukansu a bakin aikinsu daga kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Alkaluman baya-bayan nan, da aka tattara, sun nuna cewa ‘yan sanda 581 da soji 384 ne suka mutu a bakin aikinsu a cikin shekarun.

Tsoffin manyan hafsoshin tsaron da suka kwatanta lamarin da abin takaici, inda suka ce hakan ba zai yi tasiri wajen rage kwarjinin jami’an tsaro da ke aiki a wurare daban-daban na kasar ba.

No comments