Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya jagoranci rushe wasu gine-gine a kewayen filin sukuwa dake Anguwar Nassarawa a daren jiya Juma...
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya jagoranci rushe wasu gine-gine a kewayen filin sukuwa dake Anguwar Nassarawa a daren jiya Juma'a, wadanda aka yi lokacin Tsohuwar gwamnati.
Yayin aikin rusau din Gwamnan na tare da rakiyar kwamishinan 'yan Sandan Kano CP Muhammad Gumel da manyan jami'an gwamnati da kuma tarin jami'an tsaro.
Sabuwar gwamnatin na zargin tsohuwar gwamnati da sayar da filayen gwamnati da al'umma ke amfana tare da kuma gine-gine ba bisa ka'ida ba.
No comments