Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaben ƙananan Hukumomi A Bauchi: Ƙananan yara sun riƙa kaɗa ƙuri'a

Zaben kananan hukumomin jihar Bauchi da aka gudanar a yau Asabar 17 ga watan Agustan 2024, ya ci karo da zarge-zargen kura-kurai da suka had...


Zaben kananan hukumomin jihar Bauchi da aka gudanar a yau Asabar 17 ga watan Agustan 2024, ya ci karo da zarge-zargen kura-kurai da suka hada da zabe daga kananan yara.

Hon. Abdulmumini Hassan, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Ningi, ya zargi jam’iyyar PDP da tafka magudi a zaben.

Da yake zantawa da manema labarai a Ningi, Hon. Abdulmumini Hassan ya nuna matukar damuwarsa, inda ya bayyana cewa an tafka kura-kurai a zaben tun kafin a bayyana sakamakon zaben.

Hakazalika wakilanmu da suka tsaya a rumfunan zabe daban-daban, sun kuma lura da yadda zaben kananan yara ya faru, da rashin bin ka’ida, da kuma rashin isar jami’an BASIEC a rumfunan zabe a kan lokaci.

An ga masu kada kuri’a ‘yan kasa da shekaru n da ya dace suna kada kuri’a ga jam’iyyar PDP a rumfunan zabe da dama da ke yankin gundumar Ningi.

Hotunan faifan bidiyo sun kuma nuna yadda yara kanana ke kada kuri'a a rumfunan zabe na Maciya, Babban Sakatariyar zabe na Makarantar Firamare, da Bunusai Polling Unit da ke Ningi West da Ningi East Wards.

Ga wasu kadan daga cikin hotunan yadda kananan yara ke kada kuri'a: 











No comments