Daga A'isha Suleiman Zariya Kamar yadda uwar jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta fitar da tsari na gudanar da zaɓukan 'yan takarar kuj...
Kamar yadda uwar jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta fitar da tsari na gudanar da zaɓukan 'yan takarar kujerar shugabanin kananan hukumomi a ranar 16 ga watan Agusta na 2024 an sami nasarar gudanar da na karamar hukumar Kudan na jihar Kaduna lafiya.
Wakilinmu ya shaida yadda zaben ya gudana a garin Hunkuyi. Zaben an gudanar da shi ne a babban makarantar Firamare ta Hunkuyi. Bayan da dukkan masu iko na kwamitin shirya zaben suka hallara a wajen kaɗa kuri'ar ne aka shelanta cewa duk mazabu su shirya su bi layi don tantance duk wani mai kuri'a.
Bayan tantancewar ne sai malaman zaben suka bayar da ikon kaɗa kuri'ar.
Mista Samuel Kura ne malamin zaben kuma shi ne ya shelanta Honorabul Dauda Iliya a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 223 bayan ƙirga kuri'un.
Mista Samuel ya ce, "Gaba ɗaya kuri'un guda 229 ne kuma guda 6 ne suka lalace guda 223 ne suka zama tabbatattun kuri'u da Honorabul Dauda Iliya ya samu kuma hakan ya mai da shi cikakken dan takarar shugaban karamar hukumar Kudan a jam’iyyar APC a yanzu haka" in ji shi.
Bayan kammala zaben ne sai ɗan takarar kujerar shugaban karamar ta Kudan din Honorabul Dauda Iliya ya zanta da manema labarai.
Dan takarar ya ce " Na godewa Allah maɗaukakin sarki da ya bamu wannan nasara bisa haka zan yi bakin kokarina wajen bayar da himma a wajan ci gaban wannan karamar hukumar da jama'armu baki ɗaya da ikon Allah" in ji shi.
Honorabul Dauda ya yi dogon jawabi na neman goyan baya ga jama'ar karamar hukumar ta Kudan da suka taru a wannan waje da sauran jama'ar dake gidajen su.
Shima tsohon Kwamishina Honorabul Magaji Hunkuyi da yake nasa jawabin bayan shelanta Honorabul Dauda a matsayin wanda ya lashe zaɓen na fidda gwani cewa ya yi,a gaskiya ba su yi zaɓen tumun dare ba kuma da ikon Allah Dauda ba zai ba jama'arsa kunya ba.
Honorabul Magaji ya ƙara da cewa dukkanin al'ummar ƙaramar hukumar Kudan za su shaida da romon siyasa da ikon Allah
Ƙarshe ya yi godiya ga dukkan ya'yan jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar ta Kudan bisa gudummawar da suka bayar.
An yi taro lafiya an gama lafiya.
No comments