An zuba sojoji a fadar Masarautar Keffi Daga Muhammad A. Dalhatu Biyo bayan rikici...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Biyo bayan rikicin da ake alakanta shi da na 'yan sara suka wadanda ake cewa 'YAN SHARA, a garin Keffi dake karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita tare da dakatar da dukkanin wani zirga-zirga da ya hada kasuwanci da aiki.
Shugaban karamar hukumar Keffi, Muhammad Baba Shehu shi ne ya ayyana dokar hana fita a karamar hukumar har sai mama ta gani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Dokar hana fitar ta soma aiki daga shida na yamma zuwa shida na safe a ranar 1 ga watan Yunin 2023.
A wata takarda da Sakataren ilimi na karamar hukumar ta Keffi ya rubutawa makarantun gwamnati da masu zaman kansu ya bayyana musu cewa a dakatar da karatu har sai sun samu sabuwar sanarwa.
Majiyarmu ta labarta mana cewa lamarin ya faru ne da misalin wajen karfe 6 na safe. Harin bom din ya shafi wani gida mai manyan dakuna biyu. Majiyar ta ce mutum biyu da ke hayan gidan sun rasa ransu.
Ya yi zargin cewa mutum biyu din nan da suka rasa ransu suna cikin jerin mutanen da DSS ke nema ruwa a jallo; "wadanda suka mutu sun fahimci DSS sun zagaye gidansu, shi ne suka zabi su dasawa kansu bom su mutu da a kama su", inji majiyar.
Sai dai kuma tun daga ranar ta Lahadi zuwa hada wannan rahoton rikicin ya ci gaba da kazancewa tsakanin wadanda ake cewa 'YAN SHARA.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce; rikicin ya soma tun daga Kan Karofi zuwa gangaren Karofi har tsohuwar kasuwa ta Kofar Hausa.
Amma ganau ya shaida mana cewa an kashe rayukan da ba a tantance ba da ya hada maza da mata. Sannan an raunata da dama tare da barnata dukiyar al'umma.
No comments