Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: A Hukumance Tinubu Ya Nada Femi Da Akume A Matsayin Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati, Sakataren Gwamnati

Rahotannin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa; shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shugaban majalisar wakilai Fem...


Rahotannin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa; shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatan fadar Gwamnati.

Tinubu har ya wala yau ya kuma naÉ—a tsohon Gwamnan Benue George Akume kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Buhari a matsayin Sakataren Gwamnatin tarayya.

Sanarwar tabbatar da nadin mukaman na fitowa jim kadan bayan kammala ganawa da gwamnonin APC a fadar gwamnati dake Abuja. 

Darakan yada labarai na fadar Gwamnatin, Abiodun Oladunjoye shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar. 

Har wala yau Tinubu ya nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati.

No comments