Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Messi Na Shirin Sanar Da Makomarsa A Kowanne Lokaci - Rahoto

  Ana ganin dai ba abin da zai fiwa Messin dadi fiye da komawa kungiyar tasa ta yarinta da ke matsayin gida gareshi tun bayan baro Argentina...

 


Ana ganin dai ba abin da zai fiwa Messin dadi fiye da komawa kungiyar tasa ta yarinta da ke matsayin gida gareshi tun bayan baro Argentina ya na da shekaru 12 da haihuwa.

Dillalan tauraron na Argentina sun shaidawa Barcelona cewa, dan wasan ba zai ci gaba da dakon tayi daga garesu ba, ba tare da ganin hakan a zahiri ba, duk da alkawarin da kungiyar ta yi masa na sake dawo da shi don taka mata leda.

Wasu bayanai sun ce Messi mai shekaru 35 ya yi fatan ci gaba da zama a Turai amma bayan matakinsa na raba gari da PSG ya na ci gaba da ganin tayi masu gwabi daga wasu nahiyoyi duk da cewa hankalin dan wasan na Turai.

Can a Saudiya kungiyar Al Hilal ce kan gaba wajen neman Messin inda mahukuntan kasar suka bayyana cewa tuni tauraron ya aminta da komawa kasar da taka leda, yayinda Inter Miami a Amurka ke sanar da shirin tarbar dan wasan.

Akwai dai bayanan da ke cewa Inter Miami na son Barcelona ta sayi dan wasan ne ita kuma sai ta karbi aron shi, sai dai kuma alamu na nuna abu ne mai wuya Messin ya amince saboda dakon tsawon lokacin da ya dauka ya na yi ba tare da tayi daga tsohuwar kungiyar tasa ba.

No comments