Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Yi Bikin Yayen Dalibai 40 Da Suka Karanci Aikin Jarida A Zariya

  Daga Zailani Mustapha  A makon da ya gabata ne aka yi bikin yaye dalibai a karo na farko na makarantar Zaria Media Academy dake Babban Dod...

 


Daga Zailani Mustapha 

A makon da ya gabata ne aka yi bikin yaye dalibai a karo na farko na makarantar Zaria Media Academy dake Babban Dodo a cikin garin Zariya ta jihar Kaduna. 

Makarantar kamar yadda wakilinmu ya labarto ta kasance ne a karkashin Zariya Media Forum dake Harkar Musulunci ta Shaikh Ibraheem Zakzaky. 

Dalibai 40 ne aka yaye wadanda suka sami horo kan aikin Jarida. Daliban sun fito ne daga yankuna daban-daban na garin Zariya da kewaye. 

Bikin ya samu halartar al'umma da dama da 'yan'uwa da abokan arziki. Taron ya kuma gudana ne a makarantar Fudiyyah dake Babban Dodo Zariya. 

Shaikh Nafiu Musa daga ofishin Sayyed Zakzaky ne ya zama babban bako mai jawabi.

Daga cikin Malaman da suka gabatar da jawabai a wurin sun hada da; Dr. Nasuru Bawa, Barista Nuraddeen Isma'il, Malam Isa Abdullahi Gidan Bako, Malam Aliyu Saleh, da kuma Shaikh Abdulhamid Bello. 

Dukkanin Malaman sun karfafa daliban akan dorawa daga inda suka tsaya, inda suka bukaci da su zurfafa karatunsu a bangaren na aikin jarida. Sannan sun nusasshe da cewa aikin jarida aiki ne na taimakon al’umma ba aiki ne na yin kudi ba. Inda suka ce duk wanda ke bukatar yin kudi da aikin jarida ya sauya bangare tun wuri. 

Bayan kammala jawaban, a karshe an rabawa daliban Satifiket, inda aka rika ba su daya bayan daya har aka kammala.




No comments