Dokubo Asari na wadannan kalamai ne a yayin wata ganawa ta musamman da sabon shugaban Najeriyar Bola Ahmad Tinubu a fadar Villa. Yayin ga...
Dokubo Asari na wadannan kalamai ne a yayin wata ganawa ta musamman da sabon shugaban Najeriyar Bola Ahmad Tinubu a fadar Villa.
Yayin ganawar sa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawar Dakubo Asari ya ce Shugaba Tinubu yayi alkawarin gudanar da bincike game da wannan zargi, musamman a rundunar sojin ruwan kasar.
Dakubo Asari ya kuma kara da cewa ya zama wajibi gwamnati ta jajirce la’akari da karfin da masu wannan sata ke da shi, inda ya ce yana da kwarin gwiwar nan ba da jimawa ba, za’a fara ganin mutane suna layi zuwa gidan yarin kuje.
Sai dai kuma bayan wannan zargi, rundunar sojin saman kasar ta kalubalance shi kan ya bayyana sunayen sojojin da suke satar man.
Ta cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce babu wata hujja da Dakubo ya rika wajen yin wannan zargin kawai dai yana kokarin kare kansa ne matsayin san a tsohon mai laifi.
No comments